Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Dubunnan Mutanen Da Suka Mutu A Dalilin Faɗan Manoma da Makiyaya

Malamai a Sashin Koyar da Kimiyyar Siyasa na Jami’ar Abuja sun koka kan irin rayuka da dukiyoyin da aka rasa a sanadiyyar faɗan manoma da makiyaya a jihohin Benue da Plateau.

Malaman sun bayyana rashin ƙoƙari daga ɓangaren gwamnati wajen ɗaukar mataki kan masu kashe-kashen a matsayin abin da ya ƙara rura wutar matsalar.

Bayanin da malaman suka fitar a ranar Juma’a ya nuna cewar, jawaban da malaman suka gabatar a wajen duba littafin da aka rubuta kan dalilan faɗan manoma da makiyaya a Arewa ta Tsakiya wanda sashin ya shirya haɗin guiwa da Gidauniyar Rosa Luxemburg sun karkata ne kan irin ƙamarin da matsalar ta yi a yankin da ma ƙasa baki ɗaya.

Ɗaya daga cikin malaman, Dr. Olowu Olagunju ya ce, matsalar rikicin a yankin Arewa ta Tsakiya, ya yi sanadiyyar mutuwar ƴan Najeriya sama da dubu 60 daga shekarar 2001 kawo yanzu.

KARANTA WANNAN: Wasu Da Ake Zargin Makiyaya Ne Sun Kai Hari Wata Makaranta, Sun Kashe Ango Da Amarya

Olagunju ya ce, matsalar faɗan manoma da makiyayan ya yaɗu a cikin jihohi 22 cikin jihohi 36 na Najeriya, inda Arewa ta Tsakiya ta ɗauki kaso mafi yawa na rikicin.

Ya ƙara da cewar, adadin mutane dubu 60 da suka mutu a dalilin rikicin, ya haura adadin waɗanda suka mutu a dalilin ta’addancin Boko-Haram.

Ya ce, a iya shekaru biyu, tsakanin 2016 da 2018, an samu mutuwar mutane dubu 3,641 a sanadiyyar kai harin ramuwa da ɓangarorin biyu suka kai wa juna.

Malamin ya nuni da cewar akwai tsananin buƙatar shiga tsakani tare da ɗaukar matakai da cikin gaggawa za a magance matsalar ta hanyar haɗa kai da sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma.