Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

EFCC Ta Tsare Tsohon Gwamnan Sokoto Tambuwal Kan Zargin Cire Biliyoyin Nairori

Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya shiga hannun hukumar EFCC inda aka yi masa tambayoyi kan zargin cire kuɗaɗen gwamnati har Naira biliyan 189 a yanayin da ya saɓa da dokar hana safarar kuɗi ta 2022.

Rahotanni sun ce Tambuwal, wanda ya shugabanci jihar daga 2015 zuwa 2023, ya isa hedikwatar EFCC da ke Abuja da misalin ƙarfe 11:30 na safe, inda aka garzaya da shi ofishin bincike.

Wata majiyar hukumar ta bayyana cewa, “Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal, yana tsare a hannunmu bisa zargin cire kuɗaɗen gwamnati ba bisa ka’ida ba har Naira biliyan 189.”

Ya ƙara da cewa cire kuɗaɗen ya saɓawa dokar hana safarar kuɗi (Prevention and Prohibition) ta shekarar 2022.

Wani jami’in hukumar da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, “Yana tsare a hedikwatar mu da ke Abuja. Bincike yana gudana.”

Mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, ya ƙi yin tsokaci kan lamarin duk da matsin lambar ƴan jarida.