Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

El-Rufai Bai Isa Ya Sa Mu Bar PDP Ba – Sule Lamido

Tsohon gwamnan Jihar Jigawa, kuma jigo a jam’iyyar PDP, Sule Lamido, ya yi watsi da gayyatar da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi wa ‘yan adawa domin su koma jam’iyyar SDP.

El-Rufai, wanda kwanan nan ya sauya sheka daga APC zuwa SDP, ya yi wannan kira ne a wata hira da BBC Hausa, inda ya bukaci manyan ‘yan adawa kamar Atiku Abubakar, Peter Obi, Rotimi Amaechi, da Rauf Aregbesola su shiga SDP.

A martaninsa, Lamido ya ce wannan kira tamkar cin mutunci ne, yana mai jaddada cewa PDP ita ce ta fara gina siyasar El-Rufai.

“Jam’iyyar da muka kafa, PDP, ita ce ta haife shi,” in ji Lamido. 

Ya kuma kara da cewa, “A da ya ce babu manya a siyasar Najeriya, amma yanzu yana gayyatar mu mu shiga SDP?”

Lamido ya kuma kalubalanci dalilin sauya shekar El-Rufai daga APC zuwa SDP, yana mai cewa shugabanci ba da fushi ake yi ba, sai da hakuri da hangen nesa.