Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai ya janye daga buƙatar zama ɗaya daga cikin ministocin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, kamar yanda jaridar PREMIUM TIMES ta gano.
Wata majiya daga Fadar Shugaban Ƙasa ta ce, El-Rufai ya faɗawa Shugaban Ƙasa Tinubu a wani zama ranar Alhamis cewar, ya haƙura da batun kasancewa minista amma zai ci gaba da bayar da gudunmawarsa wajen ci gaban Najeriya da ƴan Najeriya a matsayinsa na ɗan ƙasa.
Ya kuma bayyanawa Tinubun cewa, yana so ya mayar da hankali kan karatun digirin digirgir, PhD da yake a jami’ar da ke ƙasar Netherlands, in ji majiyar.
KARANTA WANNAN: Naɗin Ministoci 5 Kacal Daga Kudu Maso Gabas Rashin Adalci Ne – Ƙungiyar Inyamurai
Wata majiyar kuma ta daban, ta bayyanawa PREMIUM TIMES cewa, El-Rufai ya kuma gabatar da sunan Jafaru Ibrahim Sani a matsayin wanda zai maye gurbinsa a cikin ministocin na Tinubu, inda ya ce, za a same shi nagartacce mai kuma amfani sosai.
Shi dai Jafaru Sani ya zama kwamishina na ma’aikatu uku a Jihar Kaduna da suka haɗa da Ma’aikatar Ƙananan Hukumomi, Ma’aikatar Ilimi da kuma Ma’aikatar Muhalli a lokacin El-Rufai yana gwamnan jihar.
El-Rufai na yin waɗannan maganganu ne lokacin da ya ziyarci Shugaban Ƙasa a fadarsa da ke Villa, kwana ɗaya bayan sanatoci sun tabbatar da sunayen mutane 45 domin naɗa su ministoci, inda suka cire sunan El-Rufai da na wasu mutum biyu.