
Sashen dake kula da iyakance barazanar dake tattare da bamabamai da sauran abubuwan fashewa na Majalissar Dinkin Duniya UNMAS ya tabbatar jiya laraba 5 ga wata cewa, adadin mutane 755 ne suka mutu yayin da wasu 1321 kuma suka samu raunuka sakamakon tashin bamabamai a wasu sassa na tarayyar Najeriya a cikin shekaru 6 da suka gabata.
Wadannan alkaluma suna kunshe ne cikin rahoton hadin gwiwa da sashen ya fitar tare da cibiyar tabbatar da aminci a tsakanin al’ummar Najeriya yayin bikin wannan shekara na ranar wayar da kan al’umma kan illar dasa bamabamai na MDD wanda aka gudanar a birnin Maiduguri dake arewa maso gabashin Najeriya.
Wakilin RFI HAUSA Garba Abdullahi Bagwai ya rawaito cewa, a lokacin da yake jawabi, babban jami’in kwamatin bayar da agajin jin kai ga mutanen da bala’in tashin bamabamai ya shafa na tarayyar Najeriya Group Kaftin Sadeeq Garba Shehu mai ritaya ya ce, taken bikin na bana shi ne tashin nakiya ba ya jiran lokaci muddin aka rabi inda yake.
Ya ce a sakamakon irin barazanar da bamabaman da aka binne ke haifarwa musamman ga al’ummomin da suke da karancin sani kan nau’in bamabaman, ya sa suka gabatar da shawara ga gwamnatin tarayyar kan ta yi kokarin samar da wata cibiya ta kasa da za ta rinka tafiyar da harkokin sashen na MDD dake da alhakin kawo karshen barazanar tashin bamabamai a Najeriya.
Group Kaptin Sadeeq Garba Shehu mai ritaya ya cigaba da cewa, duk da dai an samu saukin matsalolin tsaro a yankin arewa maso gabas, amma dai har yanzu akwai kalubale babba wajen dawo da dubban jama’a zuwa gonakan su domin ci gaba da noman abinci.
Ya ce, an sami adadin wadanda suka rasu da kuma wadanda suka sami raunukan ne bayan binciken da aka gudanar daga 2016, inda sakamakon binciken ya nuna cewa, a wancan lokaci ana samun mutuwar farar hula guda a kullum sakamakon tashin abubuwa masu fashewa.
Babban jami’in kwamatin bayar da agajin jin kan ga mutanen da annobar tashin bamabamai ta shafa a Najeriya ya ce har yanzu akwai wuraren noma da dama da ake da bibbinne bamabamain da ba su tashi ba a shiyyar arewa maso gabas wanda akwai bukatar a lalata su kafin cigaba da aikata filayen.
A nata jawabin ta ministar ma’aikatar harkokin jin kai da walwala da bada agaji Hajiya Sadiya Umar wadda ta sami wakilcin daraktan sashen lura da harkokin jin kai na ma’aikatar Alhaji Grema Kadi, ta ce gwamnatin tarayyar ta damu sosai wajen tabbatar da ganin ta samu nasarar kawar da dukkan al’umomin da suke yankunan da mayakan boko haram suka binne abubuwa masu fashewa.
Daga karshe shi ma daya ke tofa albarkacin bakin sa, babban darkatan cibiyar tabbatar da aminci a tsakanin al’ummar Najeriya Alhaji Abubakar Sulaiman ya ce bukatar neman gwamnatin tarayyar ta samar da cibiyar bayar da agaji kan hadarin tashin bamabamai da sauran abubuwa masu fashewa ya zama wajibi domin wadanda irin wannan tsautsayi ya shafa su rinka samun kulawar da ta kamace su cikin gaggawa.
CRI HAUSA