Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Filayen Jirgin Sama 2 Sun Yi Fice Wajen Tsari A Najeriya

Filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe na Abuja da Filin jirgin saman Port Harcourt sun samu lambobin yabo daga Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Duniya yankin Africa, ACI Africa, saboda gagarumar gudunmawarsu wajen bayar kulawar tsaron filayen jiragen da jajircewa kan martabar filayen jirage.

A yayin taron shekara-shekara karo na 33 na ACI Africa da aka gudanar a Johannesburg, Afirka ta Kudu, an bai wa waɗannan filayen jiragen sama lambobin yabo.

Tunde Moshood, mai kula da harkokin yaɗa labarai na Ministan Sufurin Jiragen Sama da Raya Sararin Samaniya ne ya bayyana hakan a wata sanarwa.

Lambobin yabon sun fito daga Sakataren Janar na ACI Africa, Ali Tounsi, da Shugaban ACI Africa, Emmanuel Chaves.

Wannan girmamawa tana nuna jajircewar ma’aikata da Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, wajen tabbatar da inganci da tsaro a filayen jiragen sama.