Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Fusatattun Ma’aikatan Shari’a Sun Garƙame Babbar Kotun Tarayya Ta Abuja Yayin Fara Yajin Aiki

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta kasance a rufe da safiyar Litinin ɗin nan, lamarin da ya bar lauyoyi, ma’aikata da waɗanda ke da shari’a cikin halin shakku da rashin samun shiga ginin kotun.

Wannan na zuwa ne duk da wata sanarwa da aka fitar a ranar Lahadi cewa ma’aikatan kotunan ba za su shiga yajin aikin da kungiyar JUSUN ta sanar ba.

Wakilin PUNCH da ya kai ziyara kotun da safe ya tarar da ƙofar a rufe gaba ɗaya, yayin da irin wannan hali ya kasance a hedikwatar Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke birnin tarayya.

A baya-bayan nan ne dai ƙungiyar ma’aikatan shari’a ta ƙasa JUSUN ta fitar da wata sanarwa mai kwanan wata 30 ga Mayu, inda ta umarci rassanta na tarayya su fara yajin aiki daga tsakar daren ranar Lahadi, 1 ga Yuni.

KARANTA WANNAN MA: Taron Masu Ruwa Da Tsaki Kan Inganta Gwamnati Da Ci Gaban Tattalin Arziƙi A Jigawa Ya Fito Da Muhimman Batutuwa

A cewar M.J. Akwashiki, muƙaddashin sakataren ƙungiyar wanda ya sanya hannu a takardar, yajin aikin na da nasaba da “kusan fashi” da ƙungiyar ke cewa an yi mata a ganawa da Ministan Ƙwadago da Ayyuka.

Daga cikin buƙatun da JUSUN ke nema akwai biyan bashin kuɗin alawus na watanni biyar, aiwatar da sabon albashin mafi ƙanƙanta na ₦70,000 da ƙarin albashi na kashi 25% zuwa 35%.

Sai dai wata sanarwa daga PRO na reshen ƙungiyar na Hukumar Shari’a ta Ƙasa (NJC), Joel Ebiloma, ta bayyana cewa kotun koli da NJC da Babbar Kotun Tarayya ba za su shiga yajin aikin ba saboda shigowar babbar alƙaliyar alƙalan Najeriya, Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, a cikin lamarin, tare da ba gwamnati wa’adin makonni biyu don warware batutuwan.