Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Ganduje Na Tsaka Mai Wuya, Sabbin Shugabannin Mazaɓarsa Sun Ƙara Dakatar Da Shi Daga APC

Rikicin da ya dabaibaye jam’iyya mai mulki, All Progressive Congress, APC a Jihar Kano ya ƙara ɗaukar sabon salo, inda sabbin waɗanda suka bayyana a matsayin shugabannin Mazaɓar Ganduje suka fitar da sabuwar sanarwar dakatara da Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje.

Sabbin shugabannin na Mazaɓar Ganduje da ke Ƙaramar Hukamar Dawakin Tofa a Jihar Kano, sun yi iƙirarin cewar sune halastattun shugabannin mazaɓar da aka zaɓa bisa doka a ranar 31 ga watan Yuli, 2021.

Da yake jawabi ga manema labarai a Kano, Sakataren Mazaɓar Ganduje, Ja’afar Adamu Ganduje wanda yai jawabi amadadin sauran shugabanni 11 na mazaɓar ya ce, dakatar da Ganduje ta zama dole saboda zarginsa da aikata laifukan yi wa jam’iyya zagon ƙasa, abinda ya jawo rarrabuwa da kuma faɗuwar jam’iyyar a zaɓuɓɓukan da suka gabata a jihar.