Ƙungiyar sa ido kan shugabanci ta Good Governance Advocates daga Jihar Jigawa ta fito fili ta kare Hon. Ibrahim Usman Kamfani Auyo, tana mai musunta rahotannin da suka bayyana a wasu kafafen yaɗa labarai cewa dan majalisar ya ce ana ba Majalisar Wakilai kuɗi daga naira miliyan ɗaya zuwa uku; ƙungiyar ta ce wannan wani kuskure ne na fassara kalaman ɗan majalissar.
Shugaban ƙungiyar Comrade Ahmed Ilallah ya ce, “mun yi nazarin videon da ke yawo a kafafen sada zumunta, kuma mun fahimci dukkanin kalamansa, wanda ko kaɗan bai saɓawa ƙa’ida ba.”
Ilallah ya ƙara da cewa ainihin maganar Kamfani ba ta nufin Majalisa ce ake bi da kuɗin, amma magana ce a kan wasu da ke biyan masu rubuta daftarin ƙudiri domin a shigar musu a majalisa, “a na kashe kuɗaɗe ba wai Majalissar a ke bawa ba, magana ce a kan duk wanda yake so a rubuta masa daftarin ƙudirin…”
Ƙungiyar ta nuna baƙin ciki da yadda, a cewarsu, “wasu kafafen yaɗa labarai suka karkatar da maganar domin wani dalili na ƙashin kan su”, tana mai cewa irin wannan sauya lafazi zai iya jawo haɗari ga martabar ɗan majalisar da kuma gaskiyar aikin yaɗa labarai.
Good Governance Advocates ta yi gargaɗin cewa, “sauya wannan kalamai bisa dalili na ƙashin kai, ba kawai zai rage darajar wannan Ɗan Majalissa bane kaɗai, hatta mutanen mazaɓar da ya fito,” kuma hakan na iya zubar da mutuncin majalisa da demokaraɗiyya baki ɗaya.
A dalilin haka ƙungiyar ta buƙaci kafafen yaɗa labarai su yi gaggawar gyara rahotannin da suka yaɗa marasa inganci, ta kuma yi kira ga ƴan jarida su koma ga asalin bidiyon kafin su yaɗa labarai masu iya haifar da tashin hankali.
Tana kuma jan hankalin jama’a, musamman a yankin Hadejia/Auyo/Kafin Hausa, cewa irin waɗannan labarai na iya raunana zumunci tsakanin wakilai da magoya bayansu idan ba a bi ƙa’ida ba.
A ƙarshe, Good Governance Advocates ta yi kira ga al’umma da su kasance masu taka-tsan-tsan da bibiyar hujjoji tare da ba da muhimmanci ga gaskiya domin kare martabar wakilai da tsarin demokaraɗiyya.