”Da an bar wannan lamari na rarraba masarautu to da wata rana sai an naɗa Sarkin Fagge, ko Kunci ko Kumbotso”, in ji shi.
Dan haka sabon sarkin ya ce ‘yan majalisa da gwamnatin sun ceto tarihi babba wanda yake haɗa kan al’umma.
Sarki Muhammad Sanusi II ya ce sarki ba ya fadanci ba ya kirari amma yana faɗar gaskiya, yana mai cewa lalle gwamnan jihar ya cika gwarzo ya kuma kara da gode wa gwamnan da al’ummar Kano.
Muhammadu Sanusi II ya ce babu wani wanda yake da wani gida a masarautar Kano duk zuri’ar Dabo ɗaya ce wanda shi ne ya kafa masarautar ta Kano.
Haka kuma sabon sarkin ya ce ba zai ce komai a kan waɗanda suka cire shi ba, saboda a cewarsa ba su isa komai ba.
BBC