Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar A. Namadi ya amince da naɗin kashin farko na masu ba shi shawara, inda ya naɗa manyan masu ba shi shawara guda biyu da kuma masu ba shi shawara guda talatin uku.
Naɗin na ƙunshe ne cikin sanarwar da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa Malam Bala Ibrahim ya sanya wa hannu a yau.
Malam Bala ya bayyana cewar, an yi naɗe-naɗen ne bisa cancanta da dacewa da kuma la’akari da hali na gari.
Ya yi fatan cewar, waɗanda aka naɗa ɗin zasu yi amfani da damar da suka samu wajen nuna kyakkyawan zaton da ake yi musu, tare da yin aiki tuƙuru wajen ganin an ciyar da Jihar Jigawa gaba.
Ya ƙara da cewar, naɗin nasu ya fara aikin nan take, yayin da yai kira gare su da su jajirce wajen cimma nasarar manufofi da tsare-tsaren gwamnati.
Waɗanda aka naɗa ɗin sune:
- Ibrahim Suleiman Gwiwa – Senior Special Adviser, Assembly Matters
- Yalwa Da’u – Senior Special Adviser, Gender Affairs
- Aliyu Hussaini Usman – Special Adviser, Inter-governmental/ Partnership
- Ibrahim Adamu Maigatari – Special Adviser, Boarder Town Affairs
- Bako Muhammad Amaryawa – Special Adviser, Farmers/Herdsmen
- Muktar Khalil – Special Adviser, Investment
- Murtala Habu Chari – Special Adviser, Youth Mobilization ( Gumel Zone)
- Abdulrahman Alkassim – Special Adviser, Local Government Affairs I
- Mujitapah Saleh Kwalam – Special Adviser, Tsangaya I
- Lawna Muhammad Garba – Special Adviser, Inter- Party Affairs
- Isah Idris Gwaram – Special Adviser, Hajj Affairs
- Muhammad Agufa Abubakar ( Maiyadi) – Special Adviser Public Mobilization ( Dutse Zone)
- Adamu Abdullahi Zabaro – Special Adviser, Livestock
- Abdulwahab T, Suleiman – Special Adviser, SEMA
- Usman Bulama – Special Adviser, Solar Power Project
- Isyaku Adamu – Special Adviser, Artisan
- Hudu Babangida Dambazau – Special Adviser, Chieftaincy Affairs (Dutse zone)
- Hamza Muhammad Hadejia – Special Adviser, Community Affairs and Inclusion
- Usman Baba Yakubu – Special Adviser, Industrial Cluster
- Adamu Gire – Special Adviser, STOWA
- Haruna Ahmad Al-Amin – Special Adviser, Export Processing Zone
- Dr. Atiku Hafizu – Special Adviser, Public Health
- Umar Imam Jahun – Special Adviser, NGOs
- Muhammad Idris Danzomo – Special Adviser, Cluster Farming
- Haladu Usman (Killer) – Special Adviser, Project Monitoring
- Lawna bn Idris – Special Adviser, Nomadic Education
- Musa Sule Dutse – Special Adviser, DCDA
- Abdullahi Mai’nasara Kazaure – Special Adviser, Microfinance Banks
- Habib Aminu Kani – Special Adviser, Technoloy/ Innovation
- Saleh Ahmad Birniwa – Special Adviser, Youth Mobilization ( Hadejia Zone)
- Abdullahi Bulama Zugo – Special Adviser, Political Mobilization (Hadejia Zone)
- Suleiman Musa Kadira – Special Adviser, Budget and Economic Planning
- Sama’ila Dawaki – Special Adviser, Chieftaincy Affairs (Hadejia Zone)
- Muhammad Sabo Yankoli – Special Adviser, Tsangaya II
- Khalid S. Ibrahim – Special Adviser, Support Groups