Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya ƙaddamar da Cibiyar Samar da Kariya ga Makarantu (Safe Schools Rapid Response Coordination Centre) a Dutse, domin ƙarfafa tsaro a makarantu.
Wannan cibiya, da aka buɗe yayin taron masu ruwa da tsaki kan tsaron makarantu, ta laƙume kuɗi kimanin naira miliyan 342.
An samar da cibiya da kayayyakin samar da tsaro na zamani, ciki har da na’urorin hange a cikin dare, na’urar GPS, da kuma fasahar sadarwa.
Haka kuma, an samar da motoci biyu kirar Toyota Hilux da babura guda huɗu domin hanzarta kai ɗauki a lokutan gaggawa.
Da yake jawabi a wajen taron ƙaddamarwar, Sufeto Janar na Ƴansanda, wanda AIG Ahmed Ammani ya wakilta, ya jinjinawa gwamnatin Jigawa kan wannan mataki.
Ya kuma gabatar da shirin IG Safe Schools Initiative, tare da jaddada mahimmancin kare ɗalibai da cibiyoyin ilimi.
Hakazalika, kwamishinan ƴansanda na Jigawa, CP A.T. Abdullahi, ya godewa Gwamna Namadi bisa tallafin da yake bayarwa, tare da kira ga ci gaba da samun haɗin kai domin tabbatar da zaman lafiya a jihar.
Taron ya tattaro manyan baƙi da masana don tattauna dabarun kare rayuka da dukiyoyin al’umma a makarantu da faɗin jihar Jigawa.