Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Gwamnan Jigawa Ya Naɗa Amirul Hajji Da Ƴan Tawagarsa

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya amince da naɗin Mai Martaba Sarkin Kazaure, Alhaji (Dr) Najib Hussaini Adamu, a matsayin Amirul Hajj kuma shugaban tawagar gwamnatin jihar don gudanar da aikin Hajji na shekarar 2025, kamar yadda wata sanarwa ɗauke da sa hannun Sakataren Gwamnatin Jiha, Malam Bala Ibrahim, ta bayyana.

Sanarwar ta kuma nuna cewa an naɗa wasu mutane hudu domin mara wa Amirul Hajj baya, waɗanda suka haɗa da Dr. Yusuf Abdurrahman, Babban Limamin Masarautar Hadejia; Alhaji Lawan Ya’u Roni, Talban Kazaure; Dr. Mahmoud Yunusa, Sa’in Dutse; da kuma Alhaji Adamu Dauda Zakar, Durbin Hadejia.

A cewar sanarwar, gwamnan ya zaɓi waɗannan mutane ne saboda hazaƙarsu, jajircewa, kishin kasa, amana, da kuma tsoron Allah da suka shahara da su.

Sakataren gwamnatin ya taya sabbin zaɓaɓɓun mambobin murna tare da buƙatar su kasance jakadu na gari da za su tabbatar da gaskiya da adalci a yayin gudanar da ayyukansu.

An umurci tawagar Amirul Hajj da su haɗa hannu da Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa da sauran hukumomi a matakin jiha, tarayya, da na ƙasa da ƙasa domin samun ingantaccen tsarin tafiyar da aikin Hajjin.

Sanarwar ta bayyana cewa naɗin ya fara aiki ne daga ranar da aka sanar da shi (wato yau), kuma ana sa ran waɗanda aka naɗa za su tabbatar da cika burin gwamnati da jama’ar jihar Jigawa.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da shirye-shiryen aikin Hajjin bana ke ƙara kankama a faɗin ƙasar nan.