Hukumar Kula da Ayyukan Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya (FCSC) ta fitar babban gargaɗi ga ma’aikata 3,598 da suka ƙi zuwa tantancewa a 2021, tana mai cewa duk wanda ya sake ƙin zuwa wannan lokaci za a ɗauka yana da takardun bogi ne.
Wannan sake tantancewar, wadda za ta gudana daga Litinin 18 ga Agusta zuwa Alhamis 28 ga Agusta, 2025, za ta shafi ma’aikatun gwamnati da dama ciki har da na Noma, Tsaro, Ilimi, Shari’a, Ayyuka, Yaɗa Labarai, Kimiyya da Fasaha, Jiragen Sama, Kuɗi, Cikin Gida da Fadar Shugaban Ƙasa.
A wata takarda da aka gani mai ɗauke da kwanan wata 4 ga Agusta, an umurci dukkan waɗanda abin ya shafa su duba sunayensu a shafin yanar gizo na hukumar da na Ofishin Shugaban Ma’aikata.
“Duk wanda ya ƙi zuwa, za a ɗauka yana ɓoye gaskiya ne don kar a gano cewa takardunsa na ƙarya ne,” in ji hukumar.
Ma’aikata za su kawo asalin takardunsu da kwafi, da suka haɗa da na ƙarin girma, gazette, canjin wurin aiki, da slip na albashin Yuli 2025.
FCSC ta bayyana cewa mafi yawan waɗanda abin ya shafa suna Ma’aikatar Yaɗa Labarai (592), Ilimi (506) da Ƙwadago (440).
Hukumar ta jaddada cewa babu ƙarin lokaci, kuma “wanda bai zo ba, ya shirya fuskantar hukunci.”