Fitaccen masanin tattalin arziki kuma Shugaban kamfanin Financial Derivatives Company Limited (FDC), Bismarck Rewane, ya yi hasashen cewa ƙarin farashin fetur da ya kai kashi 50.1 cikin ɗari, daga N568 zuwa N855 a kowanne lita, zai ƙwace naira tiriliyan biyar daga hannun masu amfani da man fetur zuwa gwamnati, kuma zai ƙara talauci a fannin makamashi.
Rewane ya yi hasashen cewa sabon farashin fetur zai ƙara yawan ƴan Najeriya da ke fama da talauci zuwa mutum miliyan 168 a shekarar 2025, daga miliyan 161 a shekarar 2023.
Ya ƙara da cewa duk da cewa ƙarin farashin na iya ƙarfafa darajar naira, amma zai iya haifar da tashe-tashen hankula yayin da jama’a suka fusata da halin da ake ciki.
Rewane ya bayyana wannan hasashen ne a makon da ya gabata a wajen jawabinsa na kowane wata a makarantar kasuwanci ta Lagos Business School (LBS), inda ya ce fara samar da fetur daga matatar Dangote zai kawo sauƙi ga masu amfani da fetur ta hanyar magance matsalolin samarwa, amma farashin zai dogara da farashin ɗanyen mai na duniya.
Ya ce illar da sabon farashin fetur zai yi ga tattalin arziki da jin daɗin jama’a ya nuna cewa naira tiriliyan biyar za a ƙwace daga hannun masu amfani da fetur a miƙa wa gwamnati, lamarin da zai ƙara hauhawar farashi a watan Satumba yayin da kuɗaɗen sufuri ke ƙaruwa.
Ya kuma bayyana cewa fara samar da fetur daga matatar Dangote zai magance matsalolin samarwa da rage safarar fetur zuwa yankunan ECOWAS, amma farashin fetur a cikin gida zai dogara da farashin ɗanyen mai na duniya.
Rewane ya ƙara da cewa ƙarin samar da wutar lantarki zuwa 6,000MW daga 4,000MW cikin watanni uku zuwa shida masu zuwa zai kawo babban cigaba ga zaman lafiyar samar da wutar lantarki da tattalin arziki.
A ƙarshe, Rewane ya ce ƙaruwar samar da wutar lantarki zai jawo zuba jari daga ƙasashen waje, inganta kwanciyar hankalin tattalin arziki, da kuma ƙara yawan samar da ayyukan yi da ke haifar da bunkasar tantalin arziƙin GDP.