Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Gwamnatin Jigawa Na Kiran Manoman Shinkafa Ƴar Rani Don Su Karɓi Kayan Noma

Mai ba wa Gwamnan Jigawa, Malam Umar Namadi shawara kan harkokin noma, Alhaji Muhammad Idris Danzomo, ya buƙaci manoman shinkafa da suka samu saƙon karɓar kayayyakin shuka da su hanzarta zuwa domin karbar su a kan lokaci.

A wata ganawa da wakilin Radio Jigawa, ya bayyana cewa akwai buƙatar manoman su karɓi kayan domin fara noman shinkafa ƴar rani a kan lokaci kafin damina ta kankama.

“Muna roƙon manoma da kada su yi ƙasa a gwiwa wajen zuwa su karɓi kayan domin shuka a kan lokaci,” in ji Danzomo.

Ya ce wannan shiri da gwamna Namadi ya ɓullo da shi na daga cikin ƙoƙarin bunƙasa noman shinkafa a jihar da kuma haɓaka tattalin arziƙin manoma.

Danzomo ya jaddada cewa kayan sun haɗa da iri, taki, magungunan feshi da sauran kayayyakin da za su taimaka wajen bunƙasa amfanin gona.

A cewarsa, “waɗanda suka samu saƙon alert su gaggauta karɓa domin kada su makara da shuka.”

Ya kuma buƙaci manoman da su nuna kishin ƙasa da jajircewa wajen amfana da shirin da gwamnati ta samar domin bunƙasa rayuwarsu.