Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Ware Sama Da Naira Biliyan 300 Domin Aiwatar Da Aiyukan Cigaban Jihar

A taron Majalisar Zartaswa ta Jihar Jigawa da aka gudanar jiya Litinin, 9 ga Satumba, 2024, ƙarkashin jagorancin Gwamna Malam Umar Namadi an yanke hukuncin aiyukan aiwatar da aiyukan raya ƙasa da dama a fadin jihar.

Majalisar ta amince da bayar da kwangilar ginawa, gyara da kula da hanyoyi 45 da suka kai tsawon kilomita 835.36 a jihar inda aka ware Naira biliyan 300.4. domin kwangilolin.

An kuma amince da biyan kashi 10% na kuɗin kwangilar wanda ya kasance Naira biliyan 30 ga kamfanonin da aka ba aiyukan hanyoyin.

Wasu daga cikin hanyoyin sun haɗa da Chuwasu zuwa Zangon Maje mai tsawon kilomita 25.80, Kankare zuwa Gangara mai tsawon kilomita 24, da sauran hanyoyi kamar na Birnin Kudu zuwa Sundumina zuwa Kiyawa mai tsawon kilomita 47.40.

Har ila yau, an amince da ware Naira miliyan 871.6 domin gyaran manyan makarantun sakandare guda 42 a fadin jihar.

Majalisar ta kuma bayar da kwangilar Naira biliyan 16.03 domin gina matsugunnin dindindin na Kwalejin Kiwon Lafiya a Hadejia, gyaran Kwalejin Kiwon Lafiya a Jahun, da gina sababbin asibitoci a Kafin Hausa da Ringim.

An kuma amince da biyan Naira biliyan 4.8 ga kamfanonin da aka ba kwangilolin don su fara aikin kai tsaye.

Haka kuma, an amince da ware Naira miliyan 473.6 domin sabuntawa da inganta tsarin samar da ruwan famfo zuwa amfani da hasken rana a garuruwa 27 da ke fadin jihar.

An bayyana cewa garuruwan da za su amfana daga wannan shirin sun hada da Dan Gaya  da ke Karamar Hukumar Sule Tankarkar, Gilima da ke Karamar Hukumar Taura, da wasu yankuna a kananan hukumomin Birnin Kudu, Kiyawa, Buji, da sauran kananan hukumomi.

Wannan shiri ya tabbatar da kudirin Gwamna Namadi na samar da ci gaba mai ɗorewa a fannin samar da ababen more rayuwa a Jigawa.