Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Gwamnatin Jigawa Ta Miƙa Dajin Baturiya Ga Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Jihar Jigawa ta miƙa Dajin Baturiya wato Hadejia Wetland Game Reserve ga Hukumar Kula da Gandun Daji ta Ƙasa (National Park Service).

A watan Yuli ne, Gwamna Mallam Umar Namadi ya karɓi baƙuncin shugabannin hukumar domin fara shirin miƙa dajin ga gwamnatin tarayyar.

Dajin Baturiya ya haɗa ƙananan hukumomi uku, wato Auyo, Kirkikasamma, da Guri, kuma yana da muhimmanci ga tattalin arziƙi, muhalli, da yawon buɗe idanu.

Shirin miƙa dajin dai ya fara ne tun shekarar 2011, amma an kammala shi a shekarar 2022 lokacin da aka sanya hannu kan takardar amincewa da miƙa dajin Baturiya da sauran dazuka guda goma a Najeriya.

Wannan miƙawa ta zama wani ɓangare na shirin Gwamnatin Tarayya na cika muradun ƙarni na Majalisar Ɗinkin Duniya, wanda zai inganta tsaro, samar da ayyukan yi, da bunƙasa tattalin arziƙi.

Ministan Muhalli ya bayyana cewa dazuka irin su Baturiya suna da matuƙar muhimmanci, kuma za a yi amfani da fasahar zamani wajen kula da su.

An kuma haɗa hannu da Bankin Duniya ta shirin ACReSAL domin samar da kayan aiki da horar da ma’aikatan da ke kula da dajin.

Abubuwan da aka miƙa sun haɗa da ma’aikata sama da 100, gidajen ma’aikata, da sauran albarkatun da ke cikin dajin.

Gwamna Namadi ya godewa Allah bisa wannan tarihi da aka kafa na miƙa dajin, tare da yabawa kwamitin da ya jagoranci aikin.

Ya kuma tabbatar da tanadi na musamman ga al’ummar da ke zaune a yankunan da ke kusa da dajin tare da tabbatar da basu haƙƙoƙinsu kamar yanda ya kamata.