Gwamnatin Jihar Jigawa ta kammala dukkanin shirye-shirye domin gudanar da tantancewa da tabbatar da bayanan tsofaffin ma’aikata da suka yi ritaya daga aiki, domin sabunta tsarin biyan fansho yadda ya dace, a cewar Shugaban Ma’aikata na Jihar, Alhaji Muhammad K. Dagaceri.
Dagaceri ya bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harabar ofishin fansho, inda ya haɗu da shugabannin ƙungiyar tsofaffin ma’aikata ta Najeriya, reshen jihar Jigawa.
Ya ce “tantancewar ba don cin zarafin wani ba ce, sai dai domin sabunta bayanan biyan fansho da tabbatar da gaskiya da sahihanci.”
Dagaceri ya ƙara da cewa tantancewar za ta taimaka wajen gyara ƙananan kura-kuran da suka shafi fanshon tsofaffin ma’aikata cikin shekaru uku da suka wuce, domin inganta tsarin.
WANI LABARIN: Taɓarɓarewar Tsarin Gidajen Yari A Najeriya, Wani Ya Shafe Shekaru 11 A Gidan Yari Yana Jiran Shari’a
Hakazalika, ya ce wannan mataki na da alaƙa da ƙudurin gwamnatin yanzu na ƙara tabbatar da gaskiya da bin doka cikin tafiyar da mulki, kuma zai ba tsofaffin ma’aikata damar gyara bayanansu da suka ɓata.
A nasa jawabin, Akanta Janar na Jiha, Abdullahi Shehu, ya buƙaci dukkan tsofaffin ma’aikata daga ma’aikatun gwamnati, ƙananan hukumomi, da hukumomin ilimi da su halarci tantancewar bisa tsarin da aka tsara.
Hakazalika, shugaban ALGON na jiha, Farfesa Salim Abdurrahman, ta bakin shugaban ƙaramar hukumar Malam Madori, Alhaji Salisu Sani, ya tabbatar da cikakken goyon bayan shugabannin ƙananan hukumomi 27 wajen tabbatar da nasarar wannan aiki.