Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Gwamnatin Kano Ta Bayyana Yau Laraba A Matsayin Ranar Hutun Takutaha

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayyana ranar yau Laraba, 4 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutu domin nuna murna da zagayowar ranar Takutaha.

Ranar Takutaha dai, rana ce ta bakwai bayan ranar 12 ga watan Rabi’il Auwal da aka haifi Manzon Allah SallalLahu Alaihi wa Sallam, wato ranar tunawa da zagayowar ranar suna.

Sanarwar bayar da hutun na ƙunshe cikin sanarwar da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Malam Baba Dantiye ya saki a yau Laraba.

KARANTA WANNAN: Shaidar Kammala Karatun Da Tinubu Ya Miƙa Wa INEC Ta Bogi Ce, Inji Rijistaran Jami’ar Chicago

Dantiye ya ce, gwamnan ya buƙaci mutane da su yi amfani da wannan lokaci wajen kwaikwayon koyarwar Annabi Muhammadu S.A.W tare da ɗabbaƙasu a rayuwarsu.

Ya kuma yi kira gare su da su yi addu’a domin samun zaman lafiya da ci gaba a faɗin jihar da ma Najeriya baki ɗaya.

Ya kuma rufe da roƙon Allah wajen ganin an samu mafita daga tsananin da ake ciki da kuma samun damuna mai albarka da albarkar noma a lokacin rani mai zuwa.