Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Gwamnatin Kano Zata Magance Matsalar Ruwansha A Birni

Gwamnatin Jihar Kano ta ce, matsalar ƙarancin ruwan shan da ake fama da ita jihar a wasu ɓangarori na birnin jihar ta kusa zuwa ƙarshe, saboda samar da abubuwan da ake buƙata domin magance matsalar da ta yi.

Kwamishinan Albarkatun Ruwa na jihar, Dr. Ali Haruna Makoda ne ya bayyana haka ga manema labarai jiya Laraba a Kano.

Ya ce, gwamnatin jihar na yin aiki tuƙuru domin tabbatar da an sami ruwan sha cikin ƴan kwanaki masu zuwa.

Kwamishinan ya bayyana matsalar a matsayin wadda ta samo asali daga na’u’rori marassa kyau musamman a tashar samar da ruwan sha ta Tamburawa wadda ke samar da ruwan ga mafi yawan sassan birnin Kano.

Ya kuma ƙara da cewa, tsananin yanayin zafi da ake ciki, shima yana taka rawa wajen ƙarancin ruwan saboda yawan amfani da ruwan da mutane ke yi.

Ya kuma bayyana cewar, gwamnatin jihar ta shiga wata yarjejjeniya da gwamnatin Ƙasar Faransa wadda za a kashe Yuro miliyan 63.4 domin samar da tashar ruwan sha ta uku a Jihar Kano.