Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranakun Hutun Bukukuwan Babbar Sallah

Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa, ranakun Juma’a 6 da Litinin 9 ga watan Yuni na shekarar 2025 sune ranakun hutun Babbar Sallah, wato Eid-ul-Adha, kamar yadda Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin a madadin gwamnatin.

Tunji-Ojo ya taya ɗaukacin al’ummar Musulmi murnar zagayowar wannan muhimmin lokaci, inda ya buƙace su da su ci gaba da nuna halaye irin na Annabi Ibrahim (A.S) na biyayya, imani da sadaukarwa.

Ya kuma yi kira ga ƴan Najeriya da su yi amfani da wannan lokaci na Sallah wajen yin addu’a domin zaman lafiya, hadin kai da ci gaban ƙasa.

KARANTA WANNAN MA: NiMET Ta Fitar Da Hasashen Samun Ruwan Sama Da Guguwa Daga Litinin Zuwa Laraba A Sassan Najeriya

“Ministan ya tabbatar wa da ƴan Najeriya cewa sabbin shirye-shiryen sauyi da ayyuka da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke aiwatarwa a ƙarƙashin manufar ‘Sabon Fatan Najeriya’ na da nufin dawo da ƙasar kan turbar ci gaba,” in ji sanarwar.

Hakazalika, ya buƙaci al’ummar Najeriya baki ɗaya da su haɗa kai da gwamnati wajen ƙoƙarinta na farfaɗo da darajar Najeriya a idon duniya.

Tunji-Ojo ya kuma jaddada muhimmancin karrama wannan lokaci da nufin inganta kyawawan ɗabi’u da haɗin kai a tsakanin jama’a.

A cewarsa, “Muna fatan al’ummar Musulmi za su yi bikin cikin lumana da jin daɗi.”

Wannan sanarwar na zuwa ne yayin da al’umma ke ci gaba da shirin gudanar da ibadar layya da sauran al’adu da ke tattare da bikin.

Gwamnatin ta buƙaci jama’a da su tabbatar da kiyaye dokoki da ƙa’idoji yayin tafiya da gudanar da shagulgula, domin kauce wa haɗurra.

Hutun dai zai bai wa ma’aikata da ɗalibai damar hutu tare da iyalansu, yayin da ake sa ran ƙarancin zirga-zirga da aiyukan gwamnati a waɗannan ranaku.