Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Gwamnatin Tarayya Ta Sha Alwashin Kakkaɓe Ƴanbindiga Yayin Da Minista, CDS Suka Isa Sokoto

A jiya ne Gwamnatin Tarayya ta bakin Ƙaramin Ministan Tsaro, Dr. Bello Matawalle, ta sha alwashin kakkaɓe ƴanbindiga da sauran gungun masu aikata laifuka da ke addabar yankin arewa maso yamma, biyo bayan umarnin Shugaban Kasa Bola Tinubu ga sojojin haɗin gwiwar Operation Hadarin Daji.

Wannan alƙawari ya zo ne yayin da Ƙaramin Ministan Tsaro, Babban Hafsan Tsaro (CDS), Janar Christopher Musa, da wasu manyan jami’an soji suka isa jihar Sokoto jiya da nufin jagorantar farmaki kan ƴanbindiga da sauran ƴan ta’adda da ke addabar yankin arewa maso yamma.

Ministan tare da tawagarsa, wanda ta haɗa da Babban Daraktan Leken Asiri na Soji (CDI) da sauran manyan jami’an soji, sun samu tarba daga Kwamandan Runduna ta 8, Birgediya Janar I. A. Ajose, da Kwamandan Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa Maso Yamma ta Operation Hadarin Daji.

In za a iya tunawa, a ranar Juma’ar da ta gabata ne Gwamnatin Tarayya ta umarci sojojin da su koma Jihar Sokoto domin tunkarar matsalar ‘yanbindiga da ke ƙara ta’azzara, tare da ba da umarni ga CDS da ya sa ido kan ƙoƙarin kawo ƙarshen hare-haren da ‘yanbindigar ke kai wa a yankunan da abin ya shafa a arewa maso yamma.

Da yake jawabi bayan taron sirri da kwamandojin haɗin gwiwa na Operation Hadarin Daji a hedkwatar Runduna ta 8 a Sokoto, Matawalle ya bayyana cewa Ma’aikatar Tsaro za ta ba da duk goyon bayan da ake bukata da kuma ƙarfafawa ga sojojin a yakin da suke yi da ‘yan ta’adda a yankin arewa maso yamma.