Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Gwamnatin Tarayya Za ta Gina Tashoshin Mota A Jihohi 6 Kan Naira Biliyan 142

Gwamnatin Tarayya ta amince da gina sabbin tashoshin mota a kowane yanki shida na Najeriya, a kan kuɗi N142,028,576,008.17, wanda zai inganta sufuri da rage haɗura a kan manyan tituna.

Ministan Sufuri, Sanata Sa’idu Alkali, ya bayyana cewa za a gina su a Abeokuta, da Gombe, da Kano, da Lokoja, da Onitsha da Ewu a Edo, domin samar da tsari da inganta ayyukan sufuri a ƙasa.

Alkali ya ce wannan mataki na farko ne na Gwamnatin Tarayya a ɓangaren sufuri bayan aikin gina tituna, inda zai taimaka wajen rage laifuka da yaɗuwar makamai a kan manyan tituna.

Ya ƙara da cewa rashin irin waɗannan cibiyoyi ya haddasa matsaloli ga masu amfani da tituna da kuma rage jin daɗin fasinjoji.

Ministan ya ce manufar ita ce tabbatar da tsaro, jin daɗin fasinjoji da bunƙasa harkokin kasuwanci a ƙasa.

Ya bayyana cewa an gabatar da wannan buƙata ga shugaban ƙasa da Majalissar Zartarwa domin amincewa bayan nazari mai kyau na tasirin ta a ƙasa baki ɗaya.

Alkali ya ce za a gudanar da aikin ne ta hanyar kamfanin Messrs Planet Project Limited.

Wannan mataki zai baiwa gwamnati damar samar da ingantaccen sufuri, rage hadura, da tabbatar da tsaron fasinjoji.

Ya ƙara da cewa ginannun tashoshin motar za su inganta tattalin arziƙi a yankuna shida na Najeriya.