Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Gwamnatin Tarayya Za Ta Shirya Tattaunawa Kan Makomar Najeriya

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Ƴan Ƙasa, ya ce, Gwamnatin Tarayya na shirin gabatar da tattaunawa tsakanin ƴan ƙasa domin magance al’amuran da suka shafi halayya da haɗin kai.

Ya bayyana cewar, tattaunawar za ta banbanta da irin tarurruka kan kundin tsarin mulkin ƙasa da gwamnatocin baya su ka yi, inda ya ce wanda za a shirya bai shafi kundin tsarin mulki ba sai dai za a yi shi ne domin wayar da kan ƴan ƙasa.

Ya ƙara da cewar taron zai mayar da hankali ne wajen sake duban ƙasa tare da yanke hukunci kan inda ake so a je, wanda kowanne ɗan ƙasa na da hannu a ciki.

Ya ce, dukkan ƴan Najeriya akwai abun da suke tsammani daga ƙasa, sannan kuma akwai abubuwa da dama da ƴan ƙasa za su yi wa ƙasarsu, saboda haka akwai buƙatar a samu amincewa kan irin ƙasar da ake mafarkin samu.

Ministan ya bayyana cewar, za a gabatar da taron nan ba da jimawa ba, inda ya ce za a gayyaci matasa, mata, dattawa, shugabannin addinai da kuma ƙwararru waɗanda zasu haɗu kan hanyar da kowa zai bi domin ciyar da ƙasa gaba.