Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirin siyar da matatun mai guda huɗu da ke Port Harcourt, Warri, da Kaduna, a matsayin wani ɓangare na sauye-sauyen masana’antar mai.
Sunday Dare, mai ba da shawara kan harkokin yaɗa labarai ga Shugaba Bola Tinubu ne ya bayyana wannan ci gaba a shafinsa na X yana mai cewa: “Za a samu ƙaruwar tace man fetur a cikin gida ta hanyar matatun Dangote da wasu ƙanana da ake da su. Lokacin samun layin man fetur zai zo ƙarshe.”
“A Bi Dokar Masana’antar Man Fetur,” Kwararre Ya Shawarci Gwamnati
Farfesa Wumi Iledare, kwararre a tattalin arziƙin man fetur, ya gargaɗi gwamnati da ta bi dokar Petroleum Industry Act (PIA) wajen aiwatar da sayar da matatun man.
Ya ce ya kamata a ce Hukumar NNPCL ce ta yanke shawarar siyarwar, ba ƴ an siyasa ba.
Manyan Masana’antu Sun Goyi Bayan Sayarwar
Manajan Darakta na 11Plc, Tunji Oyebanji, ya nuna goyon bayansa, yana mai cewa: “Sayarwar za ta haifar da sakamako mai kyau idan aka bai wa kamfanonin da suka cancanta.”
Shugaban Centre for the Promotion of Private Enterprise (CPPE), Dr. Muda Yusuf, ya ba da shawarar amfani da tsarin NLNG, inda masu saka hannun jari masu zaman kansu za su mallaki mafi yawan hannun jari don tabbatar da inganci.
PENGASSAN Ta Yi Kira Ga Haɗin Gwiwar Jama’a da Masu Zaman Kansu
Ƙungiyar Ma’aikatan Man Fetur ta Najeriya (PENGASSAN) ta nuna damuwa kan yadda ake gudanar da tsarin sayar da matatun man.
Sakatare Janar na ƙungiyar, Lumumba Okugbawa, ya ce: “Muna so a yi amfani da tsarin NLNG, inda gwamnati za ta riƙe hannun jari kaso 49%, yayin da masu zaman kansu za su riƙe kaso 51%.”
Yanayin Matatun Mai Na Najeriya
Matatun mai hudu na ƙasar nan suna da ƙarfin tace ganga 445,000 na mai a kowace rana, amma rashin inganci da gazawar gudanarwa sun sa suna aiki ƙasa da ƙima.
Tun a baya dai, NNPCL ta riga ta gayyaci kamfanoni masu zaman kansu don su gudanar da matatun mai na Warri da Kaduna.
Tare da shirin sayarwar da ke gudana, masana da masu ruwa da tsaki suna ci gaba da bayyana ra’ayi kan hanyar da ta dace don farfaɗo da masana’antar tace mai ta Najeriya yayin da ake tabbatar da tsaron makamashi da bunƙasar tattalin arziki.