Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Gwamnatina Zata Magance Matsalar Tsaro A Najeriya – Shugaba Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce, gwamnatinsa zata tanadi abubuwan da ake buƙata domin ƙara ƙarfin jami’an tsaro da samar musu da ƙarin walwala a sabon ƙudirinta na magance matsalar tsaro da sauran abubuwan da ke da alaƙa da shi a faɗin ƙasa.

Shugaban Ƙasar wanda ya samu wakilcin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayar da tabbacin ne a jiya Asabar a wajen Faretin Yaye Ɗalibai Jami’an Ƴansanda Karo na Biyar a Makaranatar Horar da Ƴansanda ta Wudil.

KARANTA WANNAN: Sojoji Sun Kashe Ƴan Bindiga 3, Sun Ƙwato Makamai A Kaduna

Ya ce, gwamntinsa na ɗaukar matakai ƙwarara wajen ganin ta magance matsalolin tsaron da suke addabar Najeriya, inda ya ce ƙoƙarin samar da kyakkyawar alaƙa tsakanin jami’an tsaro shine abun da yake ba su tabbacin samun nasara.

Ya ƙara da cewar, gwamnatin na sanya kuɗaɗe domin samarwa da jami’an ƙarin ƙwarewa da kuma samun ingantattun kayan aiki.

Ya kuma ce, suna ƙara inganta hanyoyin samun bayanan sirri da leƙen asiri a cikin ƙasa da kuma haɗa guiwa domin samun bayanai na ƙasa da ƙasa.

Shugaban ya ƙara da cewa, gwamnatin na aiwatar da aiyukan ci gaban al’umma da bunƙasa tattalin arziƙi da nufin samar da fahimtar juna, haɗin kai da wadatar arziƙi a tsakanin al’umma.