Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Gwamnoni Sun Amince Da Cewa Ana Fama Da Yunwa A Najeriya, Sun Kuma Yabi Tinubu

Gwamnonin Najeriya a karkashin inuwar Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) sun tabbatar da cewa ana fama da yunwa a ƙasar, sannan sun jinjina wa sauye-sauyen da Shugaba Bola Tinubu ya samar.

Sun bayyana hakan ne bayan wata doguwar ganawa da suka yi a Abuja, wadda ta kai har safiyar jiya Alhamis.

Shugaban Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL), Mele Kyari, ya tabbatar wa gwamnonin cewa an cire tallafin mai baki ɗaya, kuma ya yi ƙarin bayani kan ƙalubalen kamfanin da tsare-tsarensa na rage raɗaɗin hauhawar farashin man fetur ga jama’a.

Gwamna Hope Uzodimma na Jihar Imo ya ce yana fatan za a kawo ɗauki nan ba da daɗewa ba ga ƴan Najeriya.

Ya bayyana cewa sun tattauna batutuwa da suka shafi ƙasar, ciki har da samar da cibiyar lafiya ta musamman da Bankin Afirka ya ɗauki nauyi tare da King’s College ta Landan, wadda za a yi amfani da ita don magance cututtuka daban-daban.

Haka kuma, ya tabbatar da cewa gwamnonin za su haɗa kai wajen tallafawa wannan aikin.

Shugaban hukumar DSS ya kuma gabatar da sababbin dabarun yaƙi da rashin tsaro, ciki har da garkuwa da mutane da ta’addanci.

Gwamna Uzodimma ya kuma jaddada mahimmancin gyara matatun mai na cikin gida domin rage dogaro da shigo da man fetur daga waje.

Ya ce idan aka samar da man fetur a cikin gida, za a samu ayyukan yi, rage laifuka, sannan a samu damar alfahari da kasancewar Najeriya ƙasa mai arzikin mai.