Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Hanyoyin Kulawa Da Waya A Lokacin Zafi Don Gujewa Lalacewarta

Masu wayoyin hannu na iya fuskantar wadan nan abubuwa:

1. Rashin ɗaukar caji da wuri

2. Saurin sauƙar caji, da kuma

2. Ɗaukar zafi.

Da wuya baka haɗu da irin yanayin guda ɗaya, ko biyu ko duka ukun ba.

Hanyoyin Magance Wadancan Matsaloli:

1. Ka kiyayi amfani da wayarka a cikin tsakar rana.

2. Ka rage ‘apps’ da ba ka amfani da su, musamman ma masu nauyi, ko background apps.

3. Ka kiyaye amfani da wayarka a lokacin da take caji (sai dai amfani na ɗan lokaci kaɗan).

4. Ka cire cover/condom na waya don ta sha iska (musamman a lokacin da ka ji ta ɗau ɗumi).

5. Kar kana amfani da ‘apps’ da yawa a buɗe a lokaci ɗaya sai bisa buƙata. Da zarar ka kammala amfani da wani ‘app’ a wayarka, ka rufe shi (kar ya ci gaba da function on background).

6. Streaming ko yin game, na taimakawa wajen sa waya ɗaukar zafin waya.

7. Ka riƙa ajiye wayarka a wuri mai sanyi (idan ka sami ‘deflated cooler’, ko kuma ‘pure water’ mai sanyi ka ɗora wayar a kai, za ta yi caji da wuri, amma a kula, banda mai leaking).

8. Idan zafin ya yi yawa, ka sa ta a ‘airplane mode’, ka rufe kowanne ‘app’, ko kuma ka kashe ta baki ɗaya, za ta huce da wuri.

9. Kana rage hasken screen (brigthness) daidai da buƙata.

10. Kana ƙoƙarin updating na ‘apps’ na cikin wayarka.

11. Kada ka yi amfani da camera, bluetooth, hospot, WiFi, ‘video call’ ko doguwar waya (phone call) a lokacin da wayarka ta ɗau zafi, har sai ta huce.

Ɗaukar zafin waya yana da illoli da yawa:

1. Yana sa waya yin slow wajen aiki. Musamman ga masu amfani da Pixel ko iPhone, gaba ɗaya hana komai suke, su kashe data, su rufe ‘apps’ har sai zafin ya ragu.

2. Wasu wayoyin batterynsu har bindiga yake, idan zafi  ya yi yawa.

3. Yana sa waya rashin lasting.

Idan kana amfani da Android, Phone Master yana taimaka sosai wajen cooling waya (masu Infinix, Tecno da Itel, akwai shi a kan wayarsu in-build, za kuma ka iya sauke shi a Playstore).

Daga: Aliyu M. Ahmad