Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Har Yanzu Ba A Bayar Da Umarnin Biyan Mambobin NYSC ₦70,000 Ba

Hukumar kula da masu yi wa ƙasa hidima ta NYSC ta musanta labarin da ta kira na ƙanzon kurege wanda ke zagayawa a kafafen yaɗa labarai, na cewar za a biya masu bautar ƙasa mafi ƙarancin albashi na naira 70,000.

A wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Hulɗa da Jama’a na hukumar, Eddy Megwa ya sanya wa hannu, ya ce, iyaye da sauran al’umma su sani cewar babu wani umarni da ya zo wa hukumar daga masu ba ta umarni daga gwamnati kan lamarin ƙarin alawuns ga masu hidimar ƙasa.

Sanarwar ta kuma yi bayanin cewar, masu hidimar ƙasa sun hanyoyin da aka amince da su wajen fitar da duk wata sanarwa daga hukumar, don haka ya kamata su yi watsi da labaran ƙanzon kurege.

A shekarar 2020 ne dai, NYSC ta yi ƙarin alawuns na masu hidimar ƙasa daga naira 19,000 zuwa naira 33,000 watanni bayan an sanya hannu a kan dokar mafi ƙarancin albashi ta naira 30,000.

A ƙarshen watan Yulin da ya gabata ne kuma, Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya sanya hannu kan sabuwar dokar mafi ƙarancin albashi ta naira 70,000, bayan ɗebe watanni ana tattaunawa da ɓangarorin ƴanƙwadago.