Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Har Yanzu Sanata Natasha Dakatacciya Ce – Majalissar Dattawa

Mai magana da yawun Majalisar Dattawa, Sanata Yemi Adaramodu, ya bayyana cewa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan za ta ci gaba da kasancewa cikin dakatarwar da aka yi mata har sai majalisar ta dawo daga hutun makonni biyu da take ciki.

Adaramodu ya faɗi hakan ne a wata hira da Channels Television, inda ya ce “Sanata Natasha na ci gaba da kasancewa a dakatarwar duk da hukuncin kotu da ta dogara da shi wajen yunƙurin komawa bakin aiki.”

Sanatar daga mazabar Kogi ta Tsakiya, an dakatar da ita ne a watan Maris bayan rikici da ya ɓarke tsakaninta da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, wanda ta zarga da cin zarafi, zargin da ya musanta.

A ranar Talata, 22 ga watan Yulin nan, Natasha ta yi yunƙurin shiga zauren majalisa bisa hukuncin da Mai shari’a Binta Nyako ta yanke a babbar kotun tarayya da ke Abuja.

WANI LABARIN: Makusantan Tinubu Na Ɓoye Masa Gaskiyar Abun Da Ke Faruwa A APC Da Najeriya – Adamu Garba

Sai dai jami’an tsaron majalisar sun hana ta shiga, lamarin da ya janyo cece-kuce a tsakanin ƴan jam’iyyar PDP da na APC.

A halin yanzu dai, Natasha na ci gaba da nacewa cewar, dakatarwar da aka yi mata ta saɓa da dokar majalisa da kundin tsarin mulkin ƙasa.

Har yanzu majalisar ba ta bayyana cikakken matakin da za ta ɗauka a kanta bayan hutun majalisar ya ƙare ba.

Wasu na ganin cewa taƙaddamar tsakanin Shugaban Majalisa da Sanatar za ta iya tsananta, musamman duba da yadda zarge-zargen suka shafi muhimman mutane.

Ana sa ran majalisar za ta fuskanci matsin lamba daga wasu ƴan majalisar da ƙungiyoyin fararen hula bayan hutun domin warware rikicin cikin gidan.