Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Hasashen Yanda Za A Kasance Da Ruwan Sama A Kwanaki 3 Masu Zuwa Da Bayanin Samuwar Ambaliya Daga NiMet

Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen samun ruwan sama da guguwar iska a sassan ƙasar daga Lahadi zuwa Talata.

A cewar jadawalin da aka fitar a Abuja, za a sami ruwan sama matsakaici a wasu jihohin Arewa da safe a Lahadi, sannan daga baya za a samu “guguwar iska mai ɗauke da ruwan sama” a Zamfara, Jigawa, Kano, Katsina, Sokoto, Kebbi, Yobe, Borno, Adamawa da Taraba, tare da “babbar alamar yiwuwar samun ambaliya” a Kebbi, Gombe da Bauchi.

Ga yankin tsakiyar ƙasar, NiMet ta hango samun “matsakaitan ruwan sama lokaci zuwa lokaci” a Plateau, FCT da Neja da safe, sannan da yamma “ruwan sama na ɗan gajeren lokaci” a FCT, Nasarawa, Neja, Plateau, Benue, Kwara da Kogi, inda ta yi gargaɗi kan yiwuwar samun ambaliya a Neja, Plateau, Kogi da Benue.

A Kudu, sama za ta samu giragizai da safe, sannan da yamma za a sami ruwan sama matsakaici a Enugu, Anambra, Oyo, Osun, Edo, Ondo, Ogun, Ekiti, Abia, Imo, Ebonyi, Delta, Rivers, Lagos, Bayelsa, Akwa Ibom da Cross River, tare da yiwuwar samun ambaliya a wasu sassan Osun.

Hasashen Litinin da Talata ya nuna samun guguwar iska da ruwan sama a yawancin jihohin Arewa, da ruwan sama a Arewa ta tsakiya, da kuma ruwan sama mai sauƙi a Kudu, musamman a yankunan da aka jero.

NiMet ta yi kira ga jama’a “da su guji tuƙi a lokacin ruwan sama mai nauyi,” kuma jihohin da ke cikin haɗarin ambaliya “su fara shirye-shiryen ba da agajin gaggawa musamman wuraren da aka nuna da jar alama.”

Ta kuma gargaɗi manoma “kar su zuba takin zamani ko magungunan kashe ƙwari kafin sauƙar ruwan sama,” ta ce a “rufe duk abubuwan da ke iya tashi,” a “cire na’urorin lantarki daga soket,” a “guji tsayawa ƙarƙashin manyan itatuwa,” kuma “kamfanonin jiragen sama su nemi rahoton yanayi na filayen jirage na musamman don tsare-tsaren tashi.”