Hukumomi sun bayyana cewa mutane da dama sun mutu sakamakon fashewar jirgin ruwa a ƙaramar hukumar Shiroro da ke jihar Neja jiya Asabar.
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA) ta tabbatar da afkuwar lamarin a yau Lahadi, inda ta ce jirgin kwale-kwalen na ɗauke da fasinjoji da kaya yayin da ya nufi kasuwar Kwata a Zumba.
Ibrahim Hussaini, jami’in hulɗa da jama’a na NSEMA, ya ce an ceto matuƙin jirgin da wasu ƴan cikin jirgin, ɗaya daga ciki na karɓar kulawa a Asibitin Gwamnati na Kuta.
Ya ce, har yanzu ba a tantance yawan mutanen da suka mutu ba yayin da aikin ceto da bincike ke gudana tare da haɗin gwiwar masu aikin ceton ruwa na gari da masu aikin sa kai.
WANI LABARIN: Kotu Ta Yanke Wani Muhimmin Hukunci Kan Shigar Ƴan Mata Masu Hidimar NYSC
A baya ma haɗuran jiragen ruwa na yawan faruwa a Najeriya, inda a watan Nuwamban 2024 mutane 27 suka mutu a wani hatsari makamancin haka a Kogi.
A watan da ya gabata ma wani jirgi da ke ɗauke da mutum fiye da 300 ya kife a Jihar Neja, lamarin da ya jefa al’umma cikin jimami.
Duk da dokar hana tafiya da daddare da hukumar ruwa ta ƙasa ta kafa, da dokar hana yawan ɗaukar kaya da fasinjoji fiye da kima, direbobin jiragen ruwa da ma’aikata na ci gaba da take dokokin.