Babban Daraktan Hukumar Bunƙasa Fasahar Zamani da Sadarwa, NITDA, Malam Kashifu Inuwa Abdullahi ya karbi baƙuncin tawaga ƙarƙashin jagorancin Olu,ide Balogun, Daraktan Google na Afirka ta Yamma daga kamfanin Google.
KARANTA WANNAN: Yawan Dogaro Da Bashi Ya Zo Ƙarshe A Najeriya – Tinubu
Ziyarar dai an kawo masa ne domin a ƙarfafa alaƙar da ke tsakanin NITDA da kamfanin Google domin ƙarfafar matasa da dama wajen ilimin amfani da fasahar zamani wajen bunƙasa tattalin arziƙinsu kamar dai yanda yake a shirin Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu na samar da aiyukan yi miliyan 1 ga ƴan Najeriya a fannin fasahar zamani.

