Hukumar Ƴan Sanda (Police Service Commission, PSC) ta sanar a shafinta ranar 15 ga Agusta, 2025 cewa ta sayi sabon portal na ɗaukar ma’aikata domin rarraba aikin ɗaukar ƴan sanda da tabbatar da gaskiya da adalci.
A sanarwar, hukumar ta bayyana cewa bayan taron shawarwari da wakilan jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya a Abuja, za a bai wa ma’aikatan kula da fannin ɗaukar ma’aikata na jihohi muhimmiyar dama a aikin ɗaukar ma’aikatan shekarar 2025.
PSC ta ce “sabon prtal ɗin da aka mallaka zai yi amfani a ɓangaren ɗaukar sabbin ƴan sanda da ma’aikatan hukumar, kuma yanzu haka a shirye yake, za a yi amfani da shi a ɗaukar ma’aikata na gaba.”
Shugaban hukumar DIG Hashimu Argungu rtd ya bayyana cewa “Hukumar na maraba da yin hadin gwiwa da jami’an jihohi, waɗanda sune mafiya kusanci da harkar ɗukar ma’aikata, domin tabbatar da cewa a kare haƙƙin kowa”, da yake jaddada muhimmancin samun haɗin kai da jihohi.
Hukumar ta ce za ta bai wa Ma’aikatar Harkokin Ƴan Sanda, Rundunar Ƴan Sanda ta Najeriya da Hukumar Federal Character damar shiga cikin portal domin tabbatar da sahihanci, kasancewa cikin tsari da kuma hana nuna bambanci.