Hukumar Kidaya ta Kasa, NPC, ta ce an dage kidayar yawan jama’a da gidaje ta shekarar 2023 saboda shirin mika mulki ga sabuwar gwamnati da kuma yanayin da kasa ta shiga bayan zabubbukan 2023.
Manajan Kidaya na Shekarar 2023 Kuma Daraktan NPC, Inuwa Jalingo ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Abuja a yau Lahadi.
Jalingo, wanda ya tabbatar da shirin hukumar na gudanar da aikin kidayar jama’a a shekarar 2023, ya ce NPC ta shirya yin kidayar jama’a irinsa na farko a Najeriya.
Ya ce hukumar ta samu nasara mai yawa a dukkan bangarorin shirye-shiryenta.
“Mun samar da ingantaccen tsarin kidaya irin wanda ake yayi a duniya ta hanyar na’ura.
“An siyo kimanin na’urori 450,000 kuma an rarraba su ga dukkan kananan hukumomi,” in ji shi.
Jalingo ya kara cewa, duk da haka, gwamnati na ci gaba da aikin da ya kamata, yana mai fatan gwamnati mai jiran gado zata ci gaba kan nasarorin da aka samu domin gudanar da kidayar.
Manajan kidayar ya kuma yabawa gwamnatin Buhari bisa goyon bayan da ta bayar, inda ya ce hukumar ta samu nasarar horar da malaman kidaya kusan 60,000 a fadin kasar nan.
“Duk wanda ya ce ba mu shirya ba, ya fadi hakan ne cikin jahilci,” in ji shi.
Jalingo ya jaddada muhimmancin kidayar jama’a da ke da nasaba da tsare-tsare na tattalin arzikin kasa da samar da bayanan tsara shugabantar al’umma.
Hukumar NPC dai ta dage kidayar yawan jama’a da gidaje da aka shirya yi a ranakun 3 ga Mayu zuwa 7 ga Mayu har sai sabuwar gwamnati ta duba shirin.
NAN