Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

ICC Ta Fitar Da Sammacin Kama Netanyahu, Gallant Da Deif Bisa Zargin Laifukan Yaƙi 

Kotun Hukunta Laifukan Yaki ta Duniya (ICC) ta bayar da sammacin kama Firayim Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, tsohon Ministan Tsaro Yoav Gallant, da kwamandan soja na Hamas Mohammed Deif. 

Kotun ta bayyana cewa akwai “dalilai masu ƙarfi” da ke nuna suna da alhakin aikata laifukan yaƙi da laifukan cin zarafin bil’adama yayin yaƙin Isra’ila da Hamas. 

Mai gabatar da ƙara na ICC, Karim Khan ne ya nemi wannan sammaci kan abin da ya faru a ranar 7 ga Oktoba 2023, lokacin da Hamas ta kai hari a kudancin Isra’ila, ta kashe mutum kusan 1,200 tare da kama wasu 251. 

Yaƙin da Isra’ila ta kai a Gaza ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 44,000, in ji hukumomin lafiya na Hamas. 

Kotun ta zargi Netanyahu da Gallant da aikata laifuka irin su kisa, cin zarafin jama’a, da amfani da yunwa a matsayin dabarar yaƙi. 

Shugabannin Hamas, ciki har da Deif, suna fuskantar zarge-zargen kisa, azabtarwa, da kuma kama mutane da ƙarfi. 

Ofishin Firayim Ministan Isra’ila ya yi tir da sammacin, yana mai kiransa da “cin mutunci ga Yahudawa” da kuma danganta shi da shari’ar Dreyfus. 

Hamas, a ɗaya bangaren, ta kira sammacin “wata kafa mai tarihi” tare da yin kira ga al’ummar duniya su tabbatar da aiwatar da shi. 

Ƙasashe 124 mambobin ICC, waɗanda ba su haɗa Isra’ila da Amurka ba, za su ɗauki nauyin aiwatar da wannan sammaci.