Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

IMF Ta Ce Sauye-sauyen Tattalin Arzikin Gwamnatin Tinubu Ba Sa Amfani

Wani sabon rahoton Asusun Bayar da Lamuni na Duniya (IMF) ya bayyana cewa manufofin tattalin arzikin da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta aiwatar cikin watanni 18 da suka gabata ba su haifar da sakamako mai ma’ana ba. 

Rahoton, wanda ya yi nazari kan yanayin tattalin arziƙin kasashen  nahiyar Afrika Kudu da Sahara, ya nuna cewa yayin da wasu ƙasashe kamar Côte d’Ivoire da Ghana ke samun nasara, Najeriya na cikin ƙasashen da ke ci gaba da fuskantar ƙalubale wajen cimma burin gyare-gyare. 

Mataimakiyar Darakta a IMF, Catherine Patillo, ta gabatar da rahoton a Lagos Business School, inda ta ce, “Fiye da kashi biyu cikin uku na kasashen sun yi gyare-gyare na kuɗaɗe, tare da samun gagarumin ci gaba a Côte d’Ivoire, Ghana, da Zambia.” 

Najeriya, duk da haka, ba ta shiga jerin ƙasashen da ke samun nasarar gyare-gyaren tattalin arzikin ba. 

Manyan Matsalolin Tattalin Arziki

Rahoton ya nuna cewa kuɗaɗen shiga na Najeriya na shekara mai zuwa za su ƙaru da kashi 3.19% amma bai kai matsakaicin na Afrika ba, wanda ya kai kashi 3.6%. 

Hauhawar farashin kaya ya tsaya a 33.8%, wanda ya fi tsanani fiye da abin da aka sanya a matsayin burin shekara, wato kashi 21%. 

Har ila yau, darajar kuɗin naira da rashin tabbas a kan farashin musayar kuɗi na ci gaba da zama babbar matsala, yayin da wasu ƙasashe suka samu ci gaba a wannan ɓangare. 

Ra’ayoyin Masu Ruwa da Tsaki

Shugaban Ƙungiyar Manoman Najeriya, Ibrahim Kabir, ya ce duk da cewa sauye-sauyen suna da mahimmanci, jinkirin aiwatar da su yana rage tasirin su. 

Haka zalika, Daraktan ActionAid Nigeria, Andrew Mamedu, ya buƙaci gwamnati da ta fi karkata ga manoman da suka dogara da ƙananan gonaki da ci gaban karkara. 

IMF ta yi kira ga Najeriya da ta fi mai da hankali wajen aiwatar da tsare-tsaren da ake da su, irin su shirin bunƙasa noma na National Agricultural Technology and Innovation Policy (NATIP), tare da yin amfani da dabarun ƙasashen da suka samu nasara don ƙara haɓaka tattalin arziƙi da samar da tsaro a ɓangaren abinci.