
Asusun ba da Lamuni na Duniya IMF ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta kare talakawa daga tasirin ƙarin farashin man fetur.
A wata hira da gidan talabijin na Arise, wakilin IMF a Najeriya, Dr. Christian Ebeke, ya bayyana cewa ana sayar da man fetur ƙasa da farashin kasuwa, wanda ke nuna yiwuwar ƙarin farashi nan gaba kaɗan.
Haka kuma, Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL) ya taba bayyana irin wannan matsayi kan farashin man fetur a Najeriya.
IMF ya nuna damuwa kan yanda ƴan Najeriya ke fuskantar tsananin wahala sakamakon manufofin gwamnati mai ci.
Dr. Ebeke ya jaddada cewa ƙara farashin man fetur ya zo ne a lokacin da ƴan Najeriya ke fama da tsadar rayuwa, hauhawar farashin abinci, da kuma bala’in ambaliya.
Ya yi kira ga gwamnati da ta ƙarfafa tsare-tsaren kariya ga talakawa domin rage musu raɗaɗin wahalhalun da suke ciki.
Ebeke ya ce shirin Gwamnatin Tarayya na tallafa wa gidaje miliyan 15 hanya ce mai kyau, amma ya kamata a ƙara sauri wajen aiwatar da shi.
A kan matsalar farashin man fetur, IMF ya ce dole ne a samar da isasshen man fetur a kasuwa domin rage dogayen layuka a gidajen mai.
Ebeke ya jaddada cewa idan ƙarin farashin man fetur ya kawo wadatar mai a kasuwa, hakan zai taimaka wajen bunkasa tattalin arziƙi da rage raɗaɗin wahala ga mutane.
IMF ya kuma yi kira da a samar da tsarin farashi na gaskiya da kuma tsare-tsaren tallafi ga masu rauni, domin su iya jure wannan mawuyacin halin.