Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ƙare gabatar da kariya a gaban kotun sauraron ƙararraƙin zaɓen gwamnan Edo ba tare da gabatar da wata shaida ba.
A ranar Talata, lauyan INEC ya sanar da kotu cewa hukumar ba za ta gabatar da shaidu ba, matakin da kotun ta amince da shi.
INEC za ta dogara ne kacokan da shaidu da kuma muhawara tsakanin jam’iyyar APC da lauyoyin Gwamna Monday Okpebholo.
Jam’iyyar PDP ce ta fara shigar da ƙara kan sakamakon zaɓen, tana zargin INEC da tafka maguɗi da wawure ƙuri’u.
Doka ta 2022 ta bai wa PDP damar mayar da hankali kan shaidun takardu, ba wai na baki ba, wanda hakan ke zama babban ginshiƙi na ƙarar da suka shigar.
Kotun ta riga ta amince da amfani da na’urorin BVAS a matsayin hujja.
Shaidun PDP sun yi iƙirarin cewa an tafka maguɗi yayin tattara sakamakon zaɓen.
A ranar Laraba, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ta ɗaga shari’ar zuwa jiya, 6 ga watan Fabrairu, sakamakon rashin zuwan shaidun INEC.