Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Isra’ila Ta Kashe Fararen Hula 92 A Gaza, Ciki Har Da Ƙananan Yara

A wani abin da ke nuna alamar cewa Isra’ila na fara aiwatar da wani sabon tsari na faɗaɗa yaƙi a Gaza, dakarunta sun kashe mutane 92 cikin daren jiya, ciki har da mata da yara ƙanana.

Wannan hari ya auku ne a wasu sassan Gaza da Isra’ila ke zargin akwai mayaƙan Hamas a cikinsu, amma rahotanni sun nuna cewa mafi yawan waɗanda suka mutu fararen hula ne.

“Dukkan matakin da muke ɗauka yana nufin kare rayuka da ƙwato fursunoninmu ne,” in ji Netanyahu a wani taro da ya gudanar bayan harin.

WANI LABARIN: Indiya Ta Ja Kunnen Pakistan, Ta Yi Barazanar Mayar Da Martani Mai Zafi

Tun kafin wannan lokaci, an daɗe ana zargin Isra’ila da yin amfani da ƙarfi fiye da kima a hare-harenta kan Gaza.

Sai dai wannan harin ya zo ne daidai lokacin da aka tabbatar akwai Yahudawa 3 da ke raye cikin Gaza, wanda hakan na nuni da matakin da Isra’ila ke shirin ɗauka don ƙwato su.

Har yanzu ba a samu wani ƙarin bayani daga gwamnatin Isra’ila ba kan musabbabin wannan hari, amma ƙasashe da dama sun fara nuna damuwa.

Harin dai ya ƙara tsananta yanayin da al’ummar Gaza ke ciki, wanda tuni suka kasance cikin matsanancin hali na tsaro da rayuwa.