Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

JAMB TA Sanar Da Wa’adin Ƙarshe Ga Jami’o’i Da Sauran Makarantu Kan Ɗaukar Ɗaliban 2025

Hukumar Joint Admissions and Matriculation Board (JAMB) ta umarci jami’o’in gwamnati a Najeriya da su kammala dukkan shirye-shiryen karɓar ɗalibai na shekarar 2025 kafin ranar 31 ga Oktoba, 2025, yayin da jami’o’in masu zaman kansu suka samu wa’adi har zuwa ranar 30 ga Nuwamba, 2025, sannan sauran makarantu su kammala kafin ranar 31 ga Disamba, 2025.

Wannan sabon jadawali, wanda hukumar ta bayyana a cikin labaranta na mako-mako a ranar Litinin, an ce ya biyo bayan shawarar taron manufofi na 2025 da Ministan Ilimi ya jagoranta domin daidaita kalandar karatu.

JAMB ta bayyana a cikin sanarwar cewa, “Duk jami’o’in gwamnati su kammala ɗaukar ɗalibai kafin ranar 31 ga October, 2025; jami’o’i masu zaman kansu su kammala kafin 30 ga November, 2025; sauran cibiyoyi su kammala kafin 31 ga December, 2025,” domin tabbatar da adalci wajen rabon guraben karatu.

Hukumar ta yi gargaɗin cewa ko da wata jami’a ba ta shirya fara sabuwar shekarar karatu ba, ya kamata ta gudanar da ɗaukar ɗalibai a kan jadawalin da aka tanada sannan ta adana bayanan, inda ta ce: “La’akari da wannan dokar, dole ne dukkan matakan shigarwa su kammala cikin lokacin da aka tanada.”

Har ila yau an umurci dukkan makarantun da ke gudanar da jarabawar post-UTME da su kammala jarabawar cikin lokacin don bin jadawalin ɗaukar ɗalibai na 2025.

Manufar wannan mataki shi ne daidaita kalandar makarantu da tabbatar da cewa ɗalibai sun samu damar guraben karatu cikin adalci a faɗin ƙasar gaba ɗaya.

JAMB ta kuma buƙaci jami’o’i da su kammala aikin ɗaukar ɗaliban tun kafin wa’adin domin kauce wa jinkiri da rikice-rikice ga ɗalibai da tsarin ilimi.