Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

JAMB Ta Ƙara Kuɗin Rijistar Jarabawa

Hukumar Shirya Jarabawar Share Fagen Shiga Jami’a, JAMB ta ƙara kuɗin rijistar yin jarabawar UTME zuwa naira 7,700 da kuma naira 6,200.

Sanarwar ƙarin kuɗin ta fito ne daga hukumar shirya jarabawar a shafinta na X, inda ta sanar da fara shirye-shiryen rijistar UTME da DE.

Sanarwar ta bayyana cewar an fara ƙirƙirar profiles ga masu son siyan jarabawar ko cike DE, sannan kuma za a fara siyar da forms a ranar Litinin 15 ga watan Janairu, 2024.

JAMB ɗin ta sanya naira 7,700 ga duk masu son yin UTME haɗe da jarabawar gwaji, yayin da ta sanya naira 6200 ga masu son yin jarabawar ba tare da jarabawar gwaji ba.

Hukumar ta kuma sanya kuɗin forms ɗin ga ƴan ƙasashen waje da ke son rubuta jarabawar a kan kuɗi dala 30.

JAMB ta kuma sanar da cewar rijisatar DE ta shekarar 2024 zata ƙare ne ranar 28 ga watan Maris, 2024 yayin da ta sanya ranar 7 ga watan Maris a matsayin ranar zana jarabawar gwaji, sai kuma ranar 10 ga watan Afrilu a matsayin ranar fitar da takardun zana jarabawar (examination slips).