Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Jami’ar Northwest, Ta Fara Ɗaukar Ɗalibai Don Shekarar Karatu Ta 2025/2026, Ta Bayyana Sharuɗɗa

Jami’ar Northwest, Sokoto, ta sanar da buɗe ɗaukar ɗalibai don shekarar karatu ta 2025/2026.

Rajistara, Alhaji Umar Mussa Garun Babba, ya ce an buɗe domin neman shiga tsangayu biyar na jami’ar.

A Tsangayar Lafiya akwai MBBS, Koyon Aikin Jinya, MLS, Radiography, Physiotherapy, Public Health da Environmental Health.

Tsangayar Kimiyya da Kwamfuta na ɗaukar masu son karanta Computer Science, Software Engineering, Cyber Security, IT, da kimiyoyi na asali.

Haka kuma akwai Tsangayar Social and Management Sciences, Education, da Law, tare da ɓangarorin koyon ilimin sadarwa da harkokin kasuwanci.

Ya ce “duk mai JAMB dole ne ya zaɓi jami’ar a matsayin zaɓi na farko kuma ya samu aƙalla maki 150,” yayin da mai DE ke buƙatar “A-level da sakamako mai kyau.”

Ya shawarci masu sha’awa su ziyarci shalkwatar jami’ar a Kalambaina ko su tuntubi Ofishin Hulda da Jama’arta.