Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Jam’iyyar APC Ta Amince Cewa Gwamnatin Tinubu Ta Sanya Ƴan Najeriya A Wahala

Jam’iyyar APC mai mulki ta amince cewa manufofin da Shugaba Bola Tinubu ya ƙaddamar sun ƙara jefa ƴan Najeriya cikin wahalhalun tattalin arziƙi.

Wannan amincewar ta fito ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na jam’iyyar, Barista Felix Morka, ya fitar yayin da yake mayar da martani ga tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa na yankin Arewa maso Yamma, Salihu Mohammed Lukman.

Lukman ya zargi jam’iyyar da rashin kyakkyawan shugabanci, inda ya bayyana cewa tsohon Shugaba Muhammadu Buhari da Shugaba Bola Ahmed Tinubu na yanzu sun kasa cika alkawurran yaƙin neman zaɓen da suka ɗauka.

Lukman ya kuma yi kira ga shugabannin jam’iyyun adawa su haɗa kai tare da yin aiki tuƙuru don kayar da gwamnatin APC a zaɓen 2027 mai zuwa.

A martaninsa, Morka ya ce Shugaba Tinubu yana ɗaukar matakai masu tsauri don sake fasalin tattalin arzikin ƙasar da aka daɗe ana fama da matsalolinsa, amma ya amince da cewa waɗannan gyare-gyare sun ƙara jefa ƴan kasa cikin wahalar tattalin arziƙi.

Morka ya ƙara da cewa rashin ɗaukar waɗannan matakai a gwamnatocin da suka gabata ne ya sa tattalin arziƙin ya ci gaba da durkushewa tsawon lokaci.

Ya kuma bayyana cewa Tinubu ba zai yi kamar shugabannin baya ba wajen barin matsalolin tattalin arziƙi ga gwamnatocin da za su zo a nan gaba, don haka zai tabbatar da kyakkyawan ci gaba mai ɗorewa.

A kan batun Lukman, Morka ya ce Lukman na neman suna ne a siyasa tun bayan ficewarsa daga matsayin mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa.