Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Jam’iyyar APC Ta Kori Mataimakin Shugaban Majalissar Dattawa

Jam’iyyar All Progressives Congress, APC, reshen Jihar Delta ta kori Mataimakin Shugaban Majalissar Dattawa, Ovie Omo-Agege, daga kasancewa dan jam’iyyar saboda zargin aikata zagon kasa ga jam’iyya da sauran laifuka da ba a bayyana ba.

Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a wata takarda mai dauke da kwanan wata 31, ga watan March, 2023.

A zaben gwamnonin da ya gabata dai, Omo-Agege ya fadi takarar da ya tsayawa jam’iyyar APC ta gwamnan Jihar Delta, inda Sheriff Oborevwori na Jam’iyyar PDP ya lashe zaben.

A zaben, Omo-Agege wanda ya samu kuri’u 240,229, kuri’un da suka gaza na wanda ya lashe zaben da kuri’u 120,005, yayinda wanda ya ci zaben ya samu kuri’u 360,234.

A takardar korar wadda Shugaban Jam’iyyar, Ulebor Isaac, a madadin Kwamitin Shugabancin Jam;iyyar na Jihar Delta, da Sakataren Jam’iyyar, Inana Michael da wasu su 23, sun hadu sun amince da korar Omo-Agege daga matsayin mamba na jam’iyyar APC kamar yanda shugabancin matsabarsa ta Orogun da kuma shugabancin jam’iyyar na Karamar Hukumar Ughelli North ya tabbatar.

Mataimakin Shugaban Majalissar Dattawan da ke cikin rikici, an kuma kalubalance shi da kin yin kokari wajen samarwa Shugaban Kasa mai Jiran Gado, Bola Tinubu kuri’u a jihar, sai dai kawai yana yiwa kansa kokarine kawai.