Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Jam’iyyar NNPP A Jigawa Ta Maka Hukumar Zaben Jihar A Kotu Kan Zaɓen Ƙananan Hukumomi

Jam’iyyar NNPP reshen Jihar Jigawa ta garzaya kotu domin neman bayani da amsoshi game da abubuwan da ta ce sun yi kama da kuskure a shirye-shiryen zaɓen ƙananan hukumomi da kansiloli da aka tsara gudanarwa ranar 5 ga watan Oktoba mai zuwa.

Tun da farko, Jam’iyyar ta nemi Hukumar Zaɓen ta sake buɗe asusun da ake tura kuɗaɗen sayan fom ɗin takarar wanda aka rufe a ƙarshen wa’adin farko da hukumar ta bayar.

Lauyan da yake kare Jam’iyyar, Barrister Kabiru Adamu, ya bayyana cewa sun nemi a buɗe asusun, amma Hukumar Zaɓen ta ƙi amincewa tare da bayyana cewa babu damar yin hakan saboda umarnin kotu na a rufe asusun.

Barrister Kabiru ya ƙara da cewa hakan ya sa suka garzaya kotu domin kare hakkin ƴan jihar, tare da yin zargin cewa Hukumar Zaɓe ta fitar da jadawalin zaben kafin gwamna ya rattaba hannu kan dokar zaɓe.

Kotun, bayan sauraren korafin, ta tambayi Babban Lauyan Gwamnatin Jiha ko suna da abin cewa kan ƙorafin na NNPP, inda ɓangaren gwamnatin ya nemi a ɗage shari’ar domin su samu damar ƙara yin nazari da rubuta amsa kan koken.

Rahotanni dai na nuni da cewa, masu son yi wa jam’iyyar ta NNPP takara a matakin shugabancin ƙaramar hukuma da kansila da dama ne ba su sami damar sayan form na takara ba har ƙarewar watan jiya, lokacin da hukumar zaɓen ta ayyana a matsayin ranar ƙarshe ta sayar da form ɗin.

A yanzu haka dai, Babbar Kotun da ke Birnin Dutse ta baiwa lauyoyin ɓangarorin biyu kwanaki goma domin komawa kotun don ci gaba da sauraren ƙarar.