Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

JAM’IYYAR PDP: Rikicin Karɓa-Karɓa A Jam’iyyar Ya Ɓarke A Taron Lagos

Shugabannin PDP daga yankin Kudu sun hallara a Lagos cikin zazzafar muhawara kan rarraba muƙamai zuwa yankunan ƙasa kafin babban taron jam’iyyar.

An yi taron da aka kira “PDP Southern Zoning Consultative Summit” inda suka haɗu da gwamnoni Seyi Makinde da Douye Diri.

Sai dai wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar a Kudu sun ƙaryata taron inda suka kira shi “ba bisa ƙa’ida ba” saboda an yi watsi da wasu manyan mutane.

An hana ƴanjarida shiga ɗakin taron kafin a fara zaman wanda aka fara da kusan ƙarfe 2:30 na rana.

Shugaban Marassa Rinjaye a Majalissar Wakilai, Kingsley Chinda, ya ce “abin takaici ne kuma abin damuwa ne cewa an kira taron ba tare da gayyatar wasu shugabanni ba.”

Ya yi gargaɗin cewa “idan aka ba wa sakamakon taron muhimmanci, za mu ɗauki mataki bisa kundin tsarin jam’iyya” don kare haƙƙin Kudu.

Rikicin ya ƙara nuna rarrabuwar kawuna a PDP yayin da ake shirin babban taron zaɓar shugabannin jam’iyyar a matakin ƙasa.