Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

JANYE TALLAFI: Jihohin Borno, Adamawa Da Yobe Sun Sauƙaƙawa Ma’aikata, Manoma Da Ɗalibai Kuɗin Hawa Mota

Gwamnatocin jihohin Borno, Adamawa da Yobe sun fara ɗaukar matakan rage raɗaɗin tsadar kuɗin mota da ya samo asali daga janye tallafin mai da Gwamnatin Tarayya ta yi.

Kamfanin Dillanci Labarai na Najeriya, NAN, ya rawaito cewa, gwamnatocin jihohin da suke da kamfanonin sufuri na kansu sun tabbatar da cewa farashin hawa motocin yana can ƙasa da wanda ake biya a tashoshin ƴan kasuwa.

A Jihar Borno, Gwamna Babagana Umara Zulum ya amince da fitar da sabbin motocin bas-bas domin tallafawa shirin rage raɗaɗin.

Mai Baiwa Gwamna Zulum Shawara a Kan Kafafen Yaɗa Labarai da Tsare-tsare, Malam Isa Gusau ya ce motocin zasu zama ƙari ne a kan waɗanda kamfanin sufuri na jihar, Borno Express Corporation ke da su.

Gusau ya kuma ce, an tanadi motoci 30 domin jigilar manoma kyauta, musamman waɗanda suke cikin birnin Maiduguri zuwa gonakinsu.

Wani ɗalibin Jami’ar Maiduguri, Mustapha Abdullahi, da wani ma’aikacin gwamnati, Ali Modu waɗanda ke amfani da motocin gwamnatin da ke ɗaukar mutane a kan naira 50 kacal sun yabawa gwamnati kan tallafawar.

Labari Mai Alaƙa: Akwai Yiwuwar Samun Ƙaruwar Tashin Farashin Fetur A Najeriya

A Jihar Adamawa ma, gwamnatin jihar da naɗa kwamiti na musamman domin fito da hanyoyin rage raɗaɗin janye tallafin man fetur, inda Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnan Jihar, Dr. Amos Edgar yake a matsayin shugaban kwamitin.

Amos ya bayyana cewa gwamnatin Adamawa zata samar motocin da zasu na jigilar ma’aikata da zirga-zirga tsakanin ƙananan hukumomin jihar cikin farashi mai sauƙi.

Ya kuma ce gwamnatin jihar ta kuma amince da baiwa ma’aikatan jihar da ƴan fansho ƙarin naira dubu goma duk wata domin rage musu raɗaɗin.

Daraktan Sufuri na Ma’aikatar Sufuri ta Adamawa, Labaran Salisu ya ce, wasu daga cikin motoci 250 da aka jinginar da rabin mallakarsu a ma’aikatar za a saka su a shirin domin jigila tsakanin ƙananan hukumomin jihar cikin araha.

A Jihar Yobe ma, Shugaban Ma’aikatar Bayar da Tallafin Gaggawa na Jiha, Dr. Mohammed Goje ya ce, akwai tsare-tsare da ake tanada domin samar da sufuri kyauta ga ma’aikata da ɗalibai a jihar.

Ya ƙara da cewa, nan ba da jimawa ba wannan shiri zai kammala, inda ma’aikata da ɗalibai zasu fara morarsa.