Adadin apps na bayar da bashi da aka goge ya ƙaru daga tara zuwa 37, kamar yanda Hukumar Kula da Haƙƙin Mai Saye da Gogayya Tsakanin Kasuwanci ta Tarayya, FCCPC, ta fitar.
Haka kuma adadin apps na bayar da bashi waɗanda gwamnati ta amince da su shima ya ƙaru daga 154 zuwa 164 kamar yanda jaridar PUNCH ta tabbatar a jiya Litinin.
Su kuma waɗanda su ke kan gwaji sun ragu daga 40 zuwa 38, yayinda waɗanda ke ƙarƙashin sanya idon gwamnati sun ƙaru daga 20 zuwa 56.
Wannan ya biyo bayan jajige apps ma su bayar da bashi da FCCPC ke yi, bayan samun ƙorafe-ƙorafen cin zarafin da ake yi wa masu karɓar bashi daga apps ɗin.
FCCPC ta bayyana cewar, apps ɗin da ta soke, an goge su gaba ɗaya daga Google Play Store.
KARANTA WANNAN: TSADAR MAI: Babu Wani Shirin Dawo Da Tallafin Mai A Najeriya, In Ji Fadar Shugaban Ƙasa
Ga sunayen apps ɗin da aka goge:
- Swiftkash App
- Hen Credit Loan App
- Cash Door App
- Joy Cash-Loan Up To 1,000,000 App
- Eaglecash App
- Luckyloan Personal Loan App
- Getloan App
- Easeloan Apps
- Naira Naija
- Cashlawn App
- Easynaira App
- Crediting App
- Yoyi App
- Nut Loan App
- Cashpal App
- Nairaeasy Gist Loan App
- Camelloan App
- Nairaloan App
- Moneytreefinance Made Easy App
- Cashme App
- Secucash App
- Creditbox App
- Cashmama App
- Crimson Credit App
- Galaxy Credit App
- Ease Cash App
- Xcredit
- Imoney
- Naira Naija
- Imoneyplus-Instant
- Nairanaija-Instant
- Nownowmoney
- Naija Cash
- Eagle Cash
- Firstnell App
- Flypay
- Spark Credit